✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osinbanjo ya bar jam’iyyar APC reshen Jihar Legas

APC reshen Jihar Legas ta ce daman bai taba kawo mata ko akwatin kofar gidansa a Legas din ba.

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya sanar da cewa ya sauya shekar mazabarsa ta jam’iyyar APC reshen Jihar Legas zuwa Jihar Ogun.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ya ayyana bukatarsa ta neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam’iyarsa ta APC mai mulki a kasar.

Wata sanarwa da Kakakin Mataimakin Shugaban Kasar, Laolu Akande, ya fitar na cewa tun a ranar 9 ga watan Janairun shekarar 2021 ne Osinbajo ya sauya mazabarsa da kuma zama mamban jam’iyar ta APC daga Legas zuwa jiharsa ta asali wato Ogun, duk dai a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Tuni dai masu lura da harkokin siyasar kasar suka ce ba su yi mamakin wannan mataki ba, ganin yadda da ma siyasar Jihar Legas ke hannun jagorancin wanda ake ganin uban gidan siyasar Osinbajo ne, wato tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A ’yan makonnin da suka gabata, shi ma Tinubu,  wanda shi ne kuma Uban Jam’iyyar APC na Kasa, ya ayyana aniyarsa ta neman takarar shugabancin kasar.

Matakin na Osinbajo na kaurace wa Legas dai, ana ganin wata dabara ce ta kauce wa adawar da zai fuskanta daga jam’iyar ta APC a jihar Legas wajen zaben fidda gwani.

Tuni dai jam’iyar APC reshen Jihar Legas ta ce ta yanke shawarar wanda za ta mara wa baya a wannan zabe mai zuwa, wanda kuma bai wuce Bola Tinubu ba.

APC reshen Jihar Legas ta yi wani gugar zana ga Osinbajo, inda ta ce ba shi da tasiri a siyasar yankin balle na kasa, hasali ma ko akwatin kofar gidansa mai 33 da ke reshe na biyu a Unguwar Victoria Garden City bai taba kawo wa APC ba a Legas.

“Wannan alamu ne na gazawa, wanda da ma ba mu yi mamaki ba domin ba [Osinbajo] shi da tasirin siyasa a Jihar Legas, balle yankin Kudu maso Yamma ko ma Najeriya,” wani mazaunin Legas ya fada wa Muryar Amurka.

Ko da yake kokarin jin ta bakin kakakin Yemi Osinbajo ya ci tura, wani mai goyon bayansa na ganin matakin da ya daukan ya dace a wannan tafiya da ya yi kama da na gudun yada kanin wani, kuma a cewar sa za su ci gaba da mara masa baya har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi a wannan tafiya.