✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Oyo: Dan takarar mataimakin Gwamna a Jam`iyar ADC ya Koma PDP

Dan takarar kujerar Mataimakin Gwamna na Jam’iyar ADC a Jihar Oyo Emmanuel Oyewole, ya sauya sheka zuwa PDP. Dan takarar ya bayyana hakan ne a…

Dan takarar kujerar Mataimakin Gwamna na Jam’iyar ADC a Jihar Oyo Emmanuel Oyewole, ya sauya sheka zuwa PDP.

Dan takarar ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a Ibadan, ranar Juma’a, in da ya ce ya sauya shekar ne domin marawa Gwamnan jihar na yanzu baya, ya sake lashe kujerarsa a 2023.

“Ni da magoya bayana mun yanke shawarar sauya sheka zuwa PDP, saboda tabbatar da dorewar cigaban da jihata ta samu.

“Magana ta gaskiya ita ce gwamnan mai ci Makinde, jagora ne na gari da ya san me yake yi, don haka za mu sake mara masa baya a zaben 2023 ya dawo karo na biyu”, in ji shi.

Ya kuma ce gwamnatin PDP sannu a hankali ta kawo cigaba jihar ta Oyo, har ta kai ta mayar da jihar inda duk mazauna cikinta ke fatan ta je.