✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Pantami ya cancanci ya zama Farfesa — Fani Kayode

Na san Pantami sosai kuma ya cancanci ya zama Farfesa.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya ce Ministan Sadarwa da Bunkasa Fasahar Tattalin Arziki, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya cancanci zama Farfesa.

Fani-Kayode, wanda ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Buhari ya fadi hakan ne cikin wani sako da ya wallafa ranar Talata a shafinsa na Twitter.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU) ta nesanta kanta daga labaran da ake yadawa kan nada Pantami a matsayin Farfesa da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) ta yi.

A kan hakan ne tsohon Ministan yake kare Pantami la’akari da yadda wasu bangarori ke sukarsa kan rashin cancantar nadinsa a matsayin Farfesa inda dama sun gabatar da hujjoji da dalilai a kan hakan.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon Ministan ya ce, “Me Pantami ya yi wa kungiyar ASUU? Yaushe irin wannan kiyayyar za ta zo karshe? Ko don yana musulmi? Na san Pantami sosai kuma ya cancanci ya zama Farfesa.

“Ya kamata soyayya ta rika shiga gaba a al’amuranmu ba wai kiyayya ba. Karya da yada labaran kanzon kurege, da bambancin addini ya janyo rarrabuwar kai a kasarmu,” a cewar tsohon Ministan.

Wasu bangaori dai sun kalubalanci nadin Pantami a matsayin, da cewa ministan bai cancanta ba tunda bai taba koyarwa a Jami’ar FUTO ba, kuma matsayin farfesa ana bayar da shi ne kawai bisa la’akari da yawan bincike, rubuce-rubuce da aikace-aikace da kuma koyarwa a aji da wanda aka ba wa ya yi.

Wani kwamiti da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) reshen Jami’ar FUTO ta kafa don binciken matsayin Farfesa da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Owerri ta ba Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ya tabbatar da sahihancin hakan.

Sai dai tuni uwar Kungiyar ASUU kasa, ta nisanta kanta da labaran da cewa ba ta yawunta Jami’ar FUTO ta yi hakan ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, har yanzu dai ana ci gaba da takaddama kan cancantar nadin mukamin Farfesa da aka yi wa Ministan.