✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya cire takunkumin sayar da sabbin layin waya

An ba da izinin ci gaba da sayar da sabbin layin waya da kuma sabuntawa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya janye takunkumin da aka sanya kan sayarwa da kuma sabunta layukan waya a Najeriya.

Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya sanar a ranar Alhamis, cewa za ci gaba da sauran abubuwan da a baya aka dakatar, muddin aka kiyaye dokokin da ma’aikatarsa da bayar na amfani da lambar NIN.

Ya za a ci gaba da yin rajistar sabbin layin ne bayan Shugaba Buhari ya amince da sabon tsarin rijistan layuka da ma’aikatar ta bullo da shi.

Ya ce tsarin ya “wajabta amfani da lambar NIN wurin yin rajistar sabon layi a ranar 14 ga Afrilu, 2021,” inji sanarwar.

Ya kara da cewa, “Sabon tsarin ya shafi sayen sabbin layin waya, bude su da kuma maye gurbinsu na kamfanoni da hukumomi da sauransu. Kuma mallakar lambar NIN sharadi ne a kowane rukuni.