Pantami ya ziyarci iyayen Hanifa a Kano | Aminiya

Pantami ya ziyarci iyayen Hanifa a Kano

Pantami ya kai wa iyayen Hanifa ziyara domin jajanta musu a Kano
Pantami ya kai wa iyayen Hanifa ziyara domin jajanta musu a Kano
    Ishaq Isma’il Musa

Ministan Sadarwa, Malam Isa Ali Pantami ya je ta’aziya Kano gidan su Hanifa Abubakar, yarinya ’yar shekara biyar da ake tuhumar wani malamin makarantarsu da laifin kisan ta.

Kamar yadda ya wassafa a shafukansa na dandalan sada zumunta, Pantami ya yi ta’aziyya ga mahaifin yarinyar, Malam Abubakar.

Haka kuma mahaifin Hanifa ya jagoranci shiga har cikin gida, inda Sheikh Pantami ya jajanta wa mahaifiya da sauran ’yan uwanta kan wannan babban rashi da suka yi.

Hotunan ziyarar da Pantami ya kai wa iyayen Hanifa domin jajanta musu a Kano

Baya ga nasihohi, Ministan ya kuma tunatar da iyayen Hanifa muhimmanci da kuma wajibcin yin hakuri a lokacin jarrabawa mai tsanani makamanciyar wannan.

Cikin sakon da ya biyo hotunan ziyarar da ya wallafa, Ministan ya roki Allah Ya sanya marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta.

Ya kuma ba wa iyayen hakuri a kan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar was azzalumai da suka nuna rashin imani.

A nasu bangaren, iyayen Hanifa sun yi godiya ga Malam da addu’ar fatan alheri a kan nasihohi da addu’o’i da ya gabatar.