✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Paul-Henri Damiba: Wane ne sabon Shugaban Burkina Faso?

Juyin mulkin ya faro ne daga boren soji a wani sansani da ake tsare da wasu masu hannu a juyin mulkin 2015.

Laftanar-Kanar din sojan da aka nada don kula da tsaron birnin Ouagadougou, fadar mulkin kasar Burkina Faso, Paul-Henri Sandaogo Damiba, ya zama sabon Shugaban Kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Christian Kabore.

An dai gabatar da Laftanar-Kanar Paul-Henri, wanda ke sanye da kakin sojoji da jar hula ne a matsayin jagoran Kungiyar Masu Kishin Kasa da Farfado da Martabar Kasar (MPSR), wacce ta kwace mulki a kasar ranar Litinin.

Wani Kyaftin din soja da ke tsaye a gefen Laftanar-Kanar Damiba ya ce, “A yau MPSR wadda ta kunshi sojoji ta yanke shawarar kawo karshen mulkin Shugaba Kabore,” kamar yadda ya karanto daga sakon Damiba a tashar talabijin Radiodiffusion Television du Burkina (RTB).

A watan Disamban 2021 ne Shugaban Kabore ya nada Damiba mai shekara 41 a matsayin Kwamandan soji a yanki na uku mafi girma a Burkina Faso, matakin da masu sharhi ke ganin yunkuri ne na lallashin sojojin domin samun karin goyon bayansu.

Kabore ya nada Damiba a mukamin mai matukar muhimmanci ne bayan wani hari da da aka mai wa jami’an tsaro a garin Inata da ke Arewacin kasar, inda aka kashe soja 49 da fararen hula hudu.

Rahotanni sun ce sojoji sun shafe kusan mako biyu ba tare da samun abinci daga gwamnati ba, lamarin da ya sa su bore da kuma neman Mista Kabore ya sauka daga mukaminsa.

Nada Laftar-Kanar Damiba ke da wuya ya yi sauye-sauye a shugabancin sojojin kasar, inda ya nada sabbin shugabanni a wasu muhimman mukamai, ya kuma sanar da shirinsa ta kawo karshen rikicin da kasar ke ciki.

Hakan wani yunkuri ne na nuna kwarewarsa wajen yakar ta’addanci, sabanin Mista Kabore, wanda sojoji ke zargi da karuwar ayyukan ta’addanci a lokacin mulkinsa.

Dimba ya samu horo a Jami’ar Sojoji da ke birnin Paris na kasar Faransa inda ya samu shaida kammala digiri na biyu a fannin nazarin aikata laifuka.

A watan Yunimn 2021 ya kaddamar da wani littafi da ya wallafa mai suna ‘Sojojin Afirka ta Yamma da Ta’addanci: Rashin Tabbas?’

Littafin nasa ya yi fashin baki a kan salon yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel da kuma gazawar dabarun yakin.

Daga 1987 zuwa 2011, Dimba ya kasance a cikin rundunar tsaron tsohon Shugaban Kasar Blaise Compaore, wanda aka yi wa juyin mulki a 2014 bayan dubban daruruwan mutanen kasar sun yi bore ga yunkurinsa na tsawaita wa’adin mulkinsa.

Daga baya gwamnatin rikon kwarya ta rushe rundunar, matakin da bai yi wa sojoji dadi ba.

A 2015, Damiba da wasu sojoji sun yi yunkurin juyin mulki, wanda ya kawar da gwamnatin rikon kwaryar na dan lokaci.

Daga baya ya bayar da shaida a kotu kan masu yunkurin juyin mulkin, ya kuma bayyana alakarsa da su.

A 2015 ya bar Burkina Faso domin karo karatu a fannin aikin soji a kasar waje.

Bayan dawowarsa aka ba shi Kwamandan rundunar 30th RCAS, mai taimaka wa kasar Burkina Faso da dabarun yaki da ta’addanci.

Ranar 3 ga watan Disamban 2021, Kabore ya ba shi alhakin kare birnin Ouagadougou daga barazanar masu tsattsauran ra’ayin addini.

Juyin mulkin ranar Litinin din, a cewar masu sharhi, ya faro ne a matsayin boren soji a wani sansani da ake tsare da wasu masu hannu a juyin mulkin 2015.