✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ba ta da makoma a Najeriya -Ngillari

Tsohon gwamnan ya ce babu wata hanya mai bullewa ga PDP da 'ya'yanta

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Bala Ngillari, ya ce jam’iyyar adawa ta PDP ta mutu, kuma ba ta da makoma a Najeriya.

Ngilari ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da ya gudana a Yola, ranar Asabar.

“Dalilin da yasa na sauya sheka daga PDP zuwa APC, shi ne saboda PDP ta mutu.

“Abu na biyu, kuma ban ga wata hanya mai billewa ga ‘ya’yan jam’iyyar ba.

“Abin da ya sa na dawo APC shi ne saboda na fuskanci ita ce za ta kai mu tudun mun tsira a kasar nan.”

Tsohon gwamnan, ya yi takarar kujerar Sanata a jam’iyyar PDP a zaben 2019, kafin komawarsa APC a 2020.

Ya kara da cewa duk mai kishin cigaban Najeriya ya kamata ya shiga jam’iyyar APC.

A cewarsa, ita ce jam’iyyar da za ta kawo mafita ga Najeriya da talakawanta.

Ngillari ya ba wa ‘yan jam’iyyar APC a Adamawa tabbacin cewa jam’iyyar ce za ta lashe kaso 90 na zaben 2023.