✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta bukaci Buhari ya yi watsi da gwamnoni kan Dokar Zabe

PDP ta bukaci Shugaba Buhari da ya yi watsi da korafin gwamnonin kasar.

’Yan Majalisar Dokokin Najeriya na babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi watsi da korafin gwamnonin kasar wajen rattaba hannu a kan sabuwar Dokar Zaben da aka yiwa gyaran fuska.

Yayin ganawa da shugabannin gudanarwar jam’iyyar su a Abuja, ’Yan Majalisun sun yi zargin cewar Gwamnonin APC na rokon shugaban da yaki sanya hannu a kan dokar wadda jama’ar kasa ke fatar ganin ta fara aiki.

Shugaban marasa rinjaye na Majalisar, Ndidi Elumelu ya roki shugaban ya sanya hannu a kan dokar domin karfafa dimokuradiya da kuma barin tarihin inganta harkokin zaben kasar.

Takaddama tsakanin Majalisar dokoki da Gwamnonin kasar ta barke lokacin da Majalisar ta amince da sabuwar dokar zabe wadda zata baiwa jama’a amfani da tsarin kato bayan kato wajen tsayar da ’yan takarar zaben kujeru daban daban.

Rahotanni sun ce matsin lamba daga gwamnonin ya sanya shugaban kasa kin sanya hannu akan dokar, abinda ya sa majalisar ta sake mata gyarar fuska, ta kuma mayar masa a ranar Litinin.