✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta bukaci Kotun ICC ta hukunta tsoffin Hafsoshin Tsaro

Jam'iyyar na neman a binciki kudadensu da kuma zargin take hakkin dan Adam.

Jam’iyyar PDP ta buakaci Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), da ta binciki Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya da suka ajiye aiki, kan laifukan cin zarafin dan Adam.

PDP ta hannun Sakataren Watsa Labaranta, Kola Ologbondiyan, ta ce ya kamata a sa wa tsoffin hafsoshin tsaron takunkumi tare da bincikar dukiyoyinsu.

Bayan kare wa’adin hafsoshin tsaron, PDP ta shigar da kara gaban Shugabar ICC, Fatou Bensouda, don bincikar su game da laifukan cin zarafi.

“PDP na bukatar a bincike su kan laifuka da suka shafi kama mutane da tsare mutane ba bisa ka’ida, kashe masu zanga-zangar lumana, da fyade da sojoji suka yi, duk a karkashin jagorancinsu.

“Ya kamata su fito su yi bayani kan irin kisan kiyashin da sojoji suka yi wa fararen hula 348 daga 2015 zuwa 2018, da kuma wanda aka yi wa masu zanga-zanga a Zariya.

“Sannan su sake bayani kan gawarwaki 347 da aka gano a wasu ramuka.

“Ya kamata ICC ta bukaci bayani kan azabtar da fararen hula a jihohin Borno, Yobe, Ribas, Abiya, da Anambra.

“Jam’iyyarmu na da hujja mai karfi kan yadda sojoji suka ci zarafin mutane yayin zanga-zangar #EndSARS,” kamar yadda jawabin jam’iyyar ya bayyana.

A ranar Talata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauya hafsoshin tsaron da sabbi.