✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta kalubalanci Buhari a kan karin kudin wuta

PDP ta ce karin kudin wutar zai iya sake jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC da su janye karin kudin wutar lantarkin da suka yi.

PDP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ta bakin Sakatarenta na Watsa Labarai, Kola Ologbondiyan, inda ta ce karin hanya ce ta gallazawa jama’a.

A cewar PDP, “Dalilan da NERC ta bayar na karun ba su wadatar ba, musamman a wannan lokaci da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki.

“PDP na jan hankalin APC da gwamnatinta cewar wannan kari ba zai haifar wa da kasar da mai ido ba, sannan zai kawo tasgaro ga harkokin kasuwanci.

“Abin da kasarmu ke bukata a wannan lokaci shi ne tsari da zai kawo sauki game sa wahalar rayuwa da ake ciki.

“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta gane cewa ‘yan Najeriya na shan wahala wajen biyan kudin wuta, dan haka bai kamata a kuma kara kudin ba.

“Jam’iyyarmu na kiran shugaban Kasa Buhari da babbar murya a kan ya yi nazari tare da bitar abin da ya dace, ba karin kudin wutar lantarki ba,” inji PDP.

Jam’iyyar ta ce ba abinda karin zai jawo face wahala da tsadar rayuwa ga talaka.