✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta kaurace wa zaben kananan hukumomin Kano

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano ta ce ba za ta shiga zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar ranar 16 ga watan Janairun 2021…

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano ta ce ba za ta shiga zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar ranar 16 ga watan Janairun 2021 ba.

PDP ta sanar da haka ne yayin wani taron ‘yan jarida da mai rikon mukamin shugaban jam’iyyar na jihar Danladi Abdulhameed a Kano ranar Talata.

Danladi, yayin taron da ya sami halartar dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Abba Kabir Yusuf ya halarta ya ce suna da amannar gwamnatin jihar ba za ta iya aiwatar da sahihin zabe ba a jihar.

A kan haka ne jam’iyyar ta ce ta yanke shawarar kaurace wa zaben domin kada ma ta bata wa kanta lokaci.

PDP ta yi zargin cewa tuni gwamnatin jihar ta shirya barnatar da kudin jihar kimanin Naira biliyan 2.3 a zaben da tuntuni suka riga suka gama shirya yadda za su gudanar da shi.

Idan za a iya tunawa, ko a shekarar 2018 dai sai da jam’iyyar PDP ta kaurace wa shiga zaben na kananan hukumomin a jihar saboda makamancin wannan zargin.