✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta kayar da Sanatan APC na Arewacin Kaduna

Ibrahim Khalil na PDP ya doke Sanata Suleiman Abdu Kwari

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Ibrahim Khalid na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lshe zaben dan Sanatan Shiyya ta Daya ta Jihar Kaduna.

Da yake sanar da sakamakon, jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Sale Alhaji Ado ya ce Ibrahim Khalid na jam’iyar PDP ya samu nasara ne da kuri’u 250,826 yayin da Sulaiman Abdu Kwari na jam’iyyar APC, wanda shi ne ke kan kujerar ya zo na biyu da kuri’u 190,008.

Kazalika Ibrahim Sidi na jam’iyyar LP ya zo na uku da kuri’u 28,418.

Ya sanar da haka ne jim kadan bayan kammala tattara zaben dan Majalisar Dattawa a ofishin INEC da ke Zariya.