✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta kori tsohon dan takararta na Gwamna a Ogun daga jam’iyyar

PDP ta ce ta kore shi ne saboda rashin da'a

Jam’iyyar PDP a Jihar Ogun, ta kori tsohon dan takarar Gwamnanta a jihar, Ladi Adebutu da wasu mutum hudu saboda rashin da’a.

Bayanin korar tasu na kunshe ne cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranar Alhamis.

Jam’iyyar ta ce, ta kori ‘ya’yan nata da lamarin ya shafa ne bisa samun su da hannu a badakalar sauya sunayen daliget yayin zaben fitar da gwani na takarar Gwamna a jihar a watan Mayun da ya gabata.

Tun farko, jam’iyyar ta dakatar da Adebutu da sauran wadanda lamarin ya shafa daga harkokin jam’iyyar tun daga ranar 25 ga Oktoba, inda aka kafa kwamitin musamman don gudanar da bincike kan batun.

Cikin sanarwar da ya fitar, shugaban kwamitin, Honarabul Akintunde Mufutau ya ce: “Bayan bincike mai zurfi kan zargin, kwamitin ya gano Adebutu da sauran sun aikata laifin da aka tuhume su.

Ya ce, don haka kwamitin ya ba da shawarar a kori wadanda lamarin ya shafa don zaman lafiyar jam’iyyar.