✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta lashe kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya

Yanzu PDP ta lashe dukkan Sanatocin Kaduna ke nan

Dan takarar Sanata a Jam’iyar PDP Lawal Adamu Usman wanda aka fi sani da Mista LA ne ya lashe kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya.

Sakamakon zaben da jami’in Zabe, Farfesa Haruna Aminu ya sanya wa hannu ya nuna Mista LA ya samu kuri’a 225,066 .

Shi kuma dan takarar Sanata na APC Abdullahi Muhammad Sani ya samu kuri’a 182,035.

Kazalika, sakamakon ya nuna dan takarar NNPP Umar Ahmad Tijjani ya samu kuri’a 24,395.

Dan takarar LP kuma, Ibrahim Muhammad Sani ya samu kuri’u 8,7510.

Da wannan sakamakon, yanzu jam’iyar PDP ce ta lashe dukkan kujerun Sanatoci uku da ke a Jihar.