✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

PDP ta lashe zaben Shugaban Karamar Hukumar Zangon Kataf a Kaduna

Francis, wanda aka fi sa ni da Zimbo, ya lashe zaben ne da kuri’a 28, 771.

Dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP  a zaben Shugaban Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna, Francis A. Sani, ya lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Francis, wanda aka fi sa ni da Zimbo, ya lashe zaben ne da kuri’a 28, 771, inda ya kayar da dan takarar APC, John Hassan, wanda ya sami kuri’a 19, 509.

Da yake sanar da sakamakon zaben sa safiyar Lahadi, Jami’in Zaben, Farfesa Nuhu Lawrence Garba, ya ce dan takarar jam’iyyar ADC, Luti Kure, ya sami kuri’a 1, 768, inda ya zo na uku.

Idan ba a manta ba, an dage zaben Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Kaduna a Kananan Hukumomin Birnin Gwari da Zangon Kataf, saboda dalilan tsaro.

A watan Satumbar da ya gabata ne dai aka gudanar da zaben a ragowar Kananan Hukumomin 21 daga cikin 23 da ke Jihar.