✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta nada Umar Damagum shugaban rikon kwarya

Kotu ta hana Ayu bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na kasa.

Kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana Iliya Umar Damagum a matsayin shugaban rikon kwarya na kasa.

Kafin nadin nasa, Damagum ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa shiyyar Arewa.

Debo Ologunagba, kakakin jam’iyyar PDP ne, ya bayyana hakan a ranar Talata a wani taron manema labarai a Abuja.

Nadin ya biyo bayan umarnin wata babbar kotu ta yi na hana Ayu bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a W.I Kpochi ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin bayan sauraron kunshin karar da aka shigar mai lamba MHC/85/2023.

Tun a ranar Juma’ar da gabata ce jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da shugabanta na kasa, Iyorchia Ayu bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.

Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke Karamar Hukumar Gboko, a Jihar Benuwe ne suka dauki matakin.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kada kuri’ar rashin kwarin gwiwa kan ayyukansa.

A lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin suka cimma, sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Vanger Dooyum ya ce zagon-kasa da Ayu da kuma na kusa da shi suka yi wa PDP ne ya janyo mata shan kaye a gundumar da kuma jihar baki daya, a zaben gwamna.

Sun kuma zargi Ayu da rashin biyan kudaden da ake karba na shekara-shekara daga ’ya’yan jam’iyyar, kamar yadda dokokinta suka tanada.