✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta soke zaben fid-da-gwanin da aka yi a Ebonyi

PDP ta ce za ta sake sanya lokacin da za a gudanar da zaben fid-da-gwanin jihar.

Jam’iyyar PDP ta soke duka zabukan fitar da gwaninta da aka yi a Jihar Ebonyi, inda ta ce za ta sanar da ranar da za a gudanar da wani sabo a nan gaba.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya fitar, inda ya ce an dauki matakin ne bayan tuntubar da aka yi tsakanin kwamitin shirya zaben jam’iyyar.

“Bayan sauraren juna da aka yi a kan lamarin kallon tsakani, kwamitin shirya zaben ya amince da a soke duka zabukan fitar da gwani da aka yi a Jihar Ebonyi.

“Da wannan muke sanar da cewa, duk wadanda aka zaba a matakin majalisar dokoki da bangaren zartarwa a Jihar Ebonyi duka an soke zaben.

“Kwamitin shirya zabuka na PDP zai sanar da sabuwar rana da za a gudanar da zabukan cikin lumana,” in ji sanarwar.

Wannan na zuwa ne makonni bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori Tochukwu Okorie a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na Ebonyi, tare da tabbatar da Silas Onu a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar.