✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta tsawaita lokacin rufe sayar da fom din takara

Za a rufe sayar da fom din neman takara ranar 9 ga Satumba, 2021

Jam’iyyar PDP ta tsawaita wa’adin rufe sayar da takardar neman tsayawa takara a zaben shugabanninta na jihohi da gundumomin da kananan hukumomi.

Sakataren Yada Labaran PDP, Kola Olagbondiyan, ya ce yanzu za a rufe sayar da fom din ne a ranar 9 ga Satumba, 2021.

Olagbondiyan ya ce jam’iyyar ta kara wa’adin ne saboda tururuwar da mabobin jam’iyyar da magoya bayanta suke yi domin samun karin bayani game da taron da ke tafe.

“Shi ya sa Majalisar Gudanarwar Jam’iyyar ta Kasa ta kara wa’adin, kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanadar.

“Jihohin da abin ya shafa su ne Adamawa, Borno, Ebonyi, Kebbi, Kwara, Legas, Oyo, Kogi (inda za a yi zaben Kananan hukumomi da na gundumomi) sai kuma Jihar Osun (inda za a yi na gundumomi).

“Ana bukatar daukacin mambobin da masu ruwa da tsaki da su lura da hakan,” inji shi.