✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

PDP ta zabi ’yar wasan kwaikwayo a takarar Mataimakiyar Gwamnan Legas

Ta sami nasarar ce bayan ta doke mutum biyar

Jam’iyyar PDP a Jihar Legas ta zabi ’yar wasan barkwancin nan a masana’antar Nollywood, Funke Akindele, wacce aka fi sani da ‘Jenifa’ a matsayin ’yar takarar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Legas a zaben 2023.

Ta sami nasarar ne bayan ta doke ragowar abokan takararta da suka nemi kujerar kusan su biyar.

Majiyoyi da dama sun ce dan takarar Gwamnan Jihar a PDP, Dokta Abdul Azeez Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor da kuma shugabancin jam’iyyar sun tabbatar da labarin.

Bayanai sun ce nan ba da jimawa ba za a bayyana kaddamar da ita a matsayin a hukumance.

Aminiya ta rawaito cewa tun da farko dai an zabi sunan mutum biyar a matsayin wadanda za a zabi daya daga cikinsu a matsayin.

Sunayen sun hada da tsohon mai neman takarar Gwamnan Jihar Gbadebo Rhodes-Vivour; tsohon dan takarar Sanata a mazabar Legas ta Gabas, Yeye Shobajo da kuma wani wanda ya taba neman takarar Gwamnan Jihar, David Kolawole Vaughan da kuma Injiniya Teslim Balogun.

Tuni dai hotunan jarumar suka fara karade gari a matsayin ’yar takarar.

Sai dai an samu matukar tirjiya daga masu ruwa da tsakin jam’iyyar tun da farko, lamarin da ya sa aka sami tsaiko a wajen fitar da sunan na karshe.

Amma daga bisani dan takarar ya shawo kan masu ruwa da tsakin kan cewa farin jinin jarumar zai taimaka wajen kara wa jam’iyyar yiwuwar yin nasara a zaben, da kuma kasancewar ta fito daga yankin Gabashin Legas.

Wata majiya da ke da kusanci da dan takarar ta tabbatar wa Aminiya zabin jarumar, kodayake ta ce ba a kai ga sanar da hakan ba a hukumance.