✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Peter Obi ne dan Najeriya mafi shahara a 2022’

Ya doke Abdussamad Rabi'u da Davido kafin ya sami nasarar

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya lashe kambun ta wanda ya fi kowa shahara a Najeriya a 2022.

Gasar dai tana samun sahalewar Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da wata kungiyar shirya fina-finan yankin, kuma za a ba da lambar girmamawar ga dukkanin wadanda suka samu nasara a cikin gasar a watan Nuwamban 2022 a Abuja.

Wannan dai  shi ne karo na hudu da kungiyoyin suka shirya makamanciyar wannan gasar, kuma ana shiryata ne a karshen kowacce shekara.

An kammala gasar ce bayan shafe tsawon sati biyu ana kada kuri’a, kuma wani gidan Talabijin mai suna Igbere TV ne ya shirya ta.

Kazalika, ’yan Najeriya na gida da ma na ketare ne suka kada kuri’a gasar ta intanet.

An dai fara tattara kuri’un ne tun daga ranar daya zuwa 14 ga watan Agustan 2022, inda sakamakon ya nuna Obin ya samu kuri’a 2,428,403, sai mai biye masa Shugaban gubgun kamfanonin BUA, Abdulsamad Isyaka Rabiu da ke da kuri’u 1,124,172.

Wanda ya samu nasarar zamowa na uku shi ne fitaccen mawakin Kudancin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido wanda ya sami kuri’a 881,766.