✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Peter Obi ya dage gangaminsa na jihohin Ekiti da Ondo

Jam'iyyar ba ta ba da bayar da cikakken bayani kan dalilin dage tarurrukan ba

Jam’iyyar LP ta ba da sanarwar dage taronta na yakin neman zaben Shugaban Kasa da ta shirya gudanarwa a jihohin Ekiti da Ondo.

jam’iyyar ta ce, ta dage tarukan ne saboda wasu dalilai da suka sha karfinta.

Ta yi alkawarin za ta sake tsayar da sabbin ranaku nan ba da dadewa ba don gudanar da taron nata a jihohin da lamarin ya shafa.

Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, jam’iyyar ta ce da farko ta so gudanar da babban taron nata ne ranar 15 ga watan Disamba a Ekiti, sannan ranar 16 a Ondo.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Peter Obi da abokin takararsa, Baba Ahmed-Datti, suka karkatar da akalar yakin neman zabensu zuwa Jihar Kogi.