✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Peter Obi ya doke Tinubu a Legas

Tinubu ya sha kaye a jiharsa a hannun Peter Obi na Jam'iyyar LP, duk da cewa kananan hukumomin da Tinubu ya lashe sun fi yawa.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, ya sha kaye a jiharsa ta Legas, a hannun abokin karawarsa na jam’iyyar LP, Peter Obi.

Obi ya kayar da Tinubu a Jihar Legas ne duk da cewa kananan hukumomin da Tinubu ya lashe sun fi yawa — amma Obi ya fi shi yawan kuri’u.

Baturiyar Zabe ta Hukumar Zabe na Kasa (INEC) a Jihar Legas, Farfesa Adenike Oladiji, ta sanar cewa Obi ya yi nasara da kuri’a 582,664 a yain da Tinubu ya zo na biyu da kuri’u 541,850.

Tinubu ya zo na biyu ne duk da cewa ya 11 daga cikin kakanan hukumo 20 na jihar da suka hada da Agege, Apapa, Badagry, Epe, Ibeju-Lekki, Ifako-Ijaiye, Ikorodu, Lagos Island, Lagos Mainland, Surulere da kuma Mushin

Obi na da tara da suka hada da Eti-Osa, Amuwo Odofin, Ikeja, Ajeromi-Ifelodun, Kosofe, Oshodi-Isolo, Alimosho, Ojo da kuma Somolu.