✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Peter Obi ya fice daga PDP

Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 72 kafin zaben fid da gwanin jam’iyyar

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, kuma tsohon dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2019, Peter Obi ya sanar da ficewa daga jam’iyyar.

Peter Obi dai, wanda ya karade jihohi da dama na Najeriya don neman goyon bayan daliget a kudurinsa na neman takarar ya fice daga jam’iyyar ne kasa da sa’o’i 72 kafin zaben fid da gwanin kujerar Shugaban Kasa.

Aminiya ta gano cewa tuni ya mika takardarsa ta ficewa daga jam’iyyar ga Shugaban PDP na mazabarsa a Jihar Anambra.

Kazalika, ya rubuta wata wasikar ga Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, a kan batun.

A cikin wasikar mai taken, “Ficewa daga jam’iyyar PDP da kuma janyewa daga neman takarar Shugaban Kasa a cikinta, Peter Obi dai bai bayyana makasudin ficewar tasa ba.

“Na rubuto maka wannan wasikar ne domin sanar da kai aniyata ta ficewa daga PDP, wacce kuma na aike wa Shugaban mazabata ta Agulu da ke Karamar Hukumar Anaocha a Jihar Anambra, daga ranar Juma’a, 20 ga watan Mayun 2022.

“Saboda haka, na janye daga neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyarka ta PDP.

“Na gode da irin karramawa da damar da aka bani a cikinta. Sai dai abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar a ’yan kwanakin nan sun sa ba zai yiwu na ci gaba da zama a cikinta ba.

“Zan ci gaba da bayar da gudummawata wajen gina kasa kamar yadda na saba,” inji Peter Obi.

Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, tsohon Gwamnan na Anambra bai fadi inda ya sa gaba ba.

Kafin komawarsa PDP, Peter Obi dan jam’iyyar APGA na kuma a cikinta ya jagoranci jihar Anambra na tsawon shekara takwas.