Pochettino ya caccaki alkalancin wasan PSG da Real Madrid | Aminiya

Pochettino ya caccaki alkalancin wasan PSG da Real Madrid

Mauricio Pochettino
Mauricio Pochettino
    Ishaq Isma’il Musa

Kocin PSG, Mauricio Pochettino ya caccaki tawagar jami’an da suka yi alkalancin karawarsu da Real Madrid a gasar Zakarun Turai zagaye na biyu.

Cikin fushi Pochettino ya tambayi dalilin da ya sa ba a yi amfani da na’urar VAR da ke taimaka wa alkalan wasan tamaula yanke hukunci ba wajen soke kwallon farko da Real Madrid ta ci, wadda ta bude kofar fitar da kungiyarsa daga gasar zakarun Turai a ranar Laraba.

A cewar Pochettino, abin kunya ne, ganin yadda Real Madrid ba ta samu nasarar jefa kwallon farko ba, sai da Benzema ya yi wa mai tsaron ragarsu Donnarumma keta, alkalan wasa kuma na gani suka yi biris da abinda ya faru.

Da fari dai zakarun na gasar Ligue 1 sun sa ran tsallakawa zuwa zagayen kwata finals bayan da Kylian Mbappe ya jefa kwallo ta biyu a ragar Madrid, amma daga bisani Benzema ya jefa musu kwallaye 3, aka tashi wasa 3-2.

Kayen da PSG ta sha a daren ranar Laraba ya sanya adadin ficewar ta daga gasar Zakarun Turai a zagayen ‘siri daya kwale’ kaiwa sau hudu bayan da suka samu nasarar a zagayen farko na karawar da suka yi a zagayen.

Tauraron Real Madrid kuma dan wasan gaba na kungiyar Karim Benzema ne ya zura kwallaye uku rigis a ragar Paris Saint Germain, kwallayen da suka yi sanadin ficewar kungiyar ta Faransa daga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana.

Real Madrid ta samu nasarar lallasa PSG ne da kuma kaiwa zuwa zagayen kwata final ne bayan rama kwallaye biyun da bakin na Faransa suka fara jefa musu a daren ranar Laraba a filin was ana Santiago Bernabeu.

A zagayen farko na karawar da suka yi a Faransa dai, PSG ce ta doke Madrid da kwallo 1-0, yayin da kuma a karawa da biyu Zakarun na La Liga suka lallasa PSG da kwallaye 3-1.

Bayan kimanin sa’a 1 da fara karawar da suka yi a daren ranar Laraba, mai tsaron ragar PSG Gianluigi Donnarumma yayi kuskuren da ya baiwa Benzama damar jefa kwallon farko.

Dan wasan gaban na tawagar kwallon kafar Faransa ya kara kwallo ta biyu da ta uku ne kuma a cikin mintuna biyu kacal, abinda ya sa aka tashi wasan Real Madrid na da jumillar kwallaye 3, PSG kuma 2.

Kwallaye ukun da Benzema ya jefawa PSG ya sanya adadin wadanda ya ci wa kungiyar tasa a jumlace kaiwa 309, inda ya wuce Alfredo Di Stefano da ya ci 308.

Kwallo ta farko da Benzema ya ci wa Real Madrid ita ce wadda ya jefa a ragar kungiyar Xeres da ke La Liga a ranar 20 ga Satumban shekarar 2009, kuma Ruud van Nistelrooy ne ya taimaka wa dan wasan a waccan lokaci.