Pogba ya soma tattaunawa da PSG, Modric zai koma City | Aminiya

Pogba ya soma tattaunawa da PSG, Modric zai koma City

Paul Pogba
Paul Pogba
    Ishaq Isma’il Musa

Dan wasan Manchester United da Faransa, Paul Pogba, ya tattauna da shugaban kungiyar Paris Saint Germain, Nasser Al-Khelaifi domin komawa kungiyar. Daily Express

Barcelona ta kyallara idanunta a kan dan wasan gaban Manchester City na kasar Spaniya, Ferran Torres mai shekara 21.

Har ma dai kocin Manchester City, Pep Guardiola ya gana da Darektan wasanni na Barcelona, Mateu Alemany  a kan dan wasan.

Ana ganin cewa komawar Ferran Torres za ta bude kofar kawo dan wasan RB Leipzig mai shekaru 23, Dani Olmo zuwa Manchester City. Manchester Evening news

Leeds United ta fara zawarcin dan wasan Real Madrid na gaba mai shekara 28, Mariano Diaz. Fichajes

Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luka Modric mai shekara 36, na sha’awar zuwa Manchester City idan kwantaraginsa ya kare a bazara. 90mins

Barcelona na sha’awar sayen dan wasan Manchester United na kasar Faransa, Anthony Martial mai shekara 25. Marca

Shi ma Ousmane Dembele, dan wasan Barcelona da Faransa, ya yi fatali da tayin tsawaita kwantaraginsa da Barcelon ta yi. Sports Mole