✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Pogba zai bar Manchester United

Pogba zai bar Manchester United bayan shafe shekara shida a kungiyar.

Manchester United ta ba da sanarwar cewa dan wasan tsakiyarta, Paul Pogba, zai bar kungiyar a karshen watan Yuni.

Paul Pogba zai raba gari da Manchester United ne da zarar kwantaraginsa ya kare a karshen wannan wata da muke ciki.

Manchester United ta sake sayen dan wasan daga Juventus a kan kudi Yuro miliyan 100, shekaru shida da suka wuce.

Dan wasan mai shekara 29, wanda ya lashe kofin duniya da tawagar ’yan wasan kasar Faransa zai bar kungiyar ne bayan gaza cimma yarjejeniya da ita.

Tuni aka fara alakanta Pogba da kungiyoyin kwallon kafa irin su Paris Saint-Germain, Real Madrid, Barcelona da kuma Manchester City.