✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pogba zai koma Juventus, Newcastle za ta yi garambawul

Asusun Zuba Jari na Saudiyya ya saye Newcastle a ranar Alhamis.

Akwai yiwuwar Juventus ta sake daukar Paul Pogba daga Manchester United, a yayin da rashin tabbas ya dabaibaye makomarsa sakamakon kwantaraginsa da zai kare a karshen kakar bana. Goal

Manchester United na shirin fara tattaunawa da Harry Maguire domin tsawaita kwantaraginsa a Old Trafford. Ana sa ran sabon kwantaragin da kungiyar za ta gabatar masa zai rika daukar fam 300,000 duk mako. Daily Mail.

Inter Milan ta kyallara idanu kan dan wasan Arsenal, Alexander Lacazette domin ya maye gurbin Alexis Sanches. Gazette dello Sport

Inter Milan tana kuma bibiyar dan wasan Real Madrid, Luka Jovic, wadanda take son dauka a watan Janairu. Gazette dello Sport

Sevilla na shige da ficen yadda za ta sayo dan kwallon Blackburn Rovers, Ben Brereton, a yayin da kuma ake alakanta dan wasanta, Youssef En-Nesyri da komawa Arsenal ko Tottenham. Team Talk

Newcastle United na son daukar dan wasan Napoli na kasar Senegal, Kalidou Koulibaly daya daga cikin jerin ’yan wasan da take son dauka. Football Insider

Newcastle tana son ganin da fara da daukar dan wasan Burnley, James Tarkowski da kuma Jesse Lingard na Manchester United wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana. Telegraph

Haka kuma Newcastle na fatan daukar dan wasan Paris St-Germain, Mauro Icardi koda yake Tottenham da kuma Juventus na son yin zawarcin dan wasan mai shekara 28. Calciomercato

Newcastle United za ta yi wannan garambawul ne ciki har da korar kocinta, Steve Bruce a makon gobe, bayan da Asusun Zuba Jari na Saudiyya ya saye kungiyar a ranar Alhamis. Mirror

Tsohon mai kungiyar Newcastle, Mike Ashley na sha’awar sayen Derby County mai buga ’yan dagaji wato Championship wadda ke fama da matsin tattalin arziki. Mirror

Liverpool ta baza komarta don ganin ta dauko Ousmane Dembele a karshen kakar bana idan kwantiraginsa ya karkare da Barcelona. Teamtalk

Leeds United tana da tabbacin cewar Kalvin Phillips zai saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar kafin karshen shekarar nan, bayan da suke kan tattaunawa. Football Insider