✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Poland ta zargi Rasha da harba mata makami mai linzami

Sai dai har yanzu ba a sana wanda ya kai harin ba

Kasar Poland na zargin Rasha da harba mata makami mai linzami a wani kauyenta da ke Gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu.

Ministan Harkokin Waje na Poland, Zbigniew Rau, ya ce, makamin ya fada ne a yankin Przewodow da ke kusa da kan iyakar kasar da Ukraine, kuma a daidai lokaci da kasar ke gudanar da wani taro kan sha’anin tsaron kasar.

Lamarin wanda ya auku ranar Talata da daddare, an ga yadda wurin da makamin ya fada ya yi kaca-kaca, sannan jami’an ceto na kokarin gudanar da aikinsu.

A cewar Shugaban Kasar Poland, Andrzej Duda, duk da dai ba su da hujja kan kasar da ta harba makamin, amma dai ya yi zargin makamin ya yi kama da kirar Rasha.

“A yanzu dai ba mu da wata kwakkwarar hujja kan wanda ya harba makamin, sai dai ya yi kama da kirar Rasha. Amma dai ana kan bincike,” inji Shugaban.

Duda ya kara da cewa, akwai yiwuwar Poland ta nemi shawarwari kan lamarin a wajen tsaron Kungiyar Kawancen Tsaro NATO da ke gudana a kasar ranar Laraba.

Tuni Ministan Harkokin Wajen Poland ya gayyaci Jakadan Rasha a kasar ya zo ya yi musu cikkaken bayani kan abin da ya faru, inji Ma’aikatar Harkokin Waje ta Poland.