✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Poland za ta ba ’yan kasa horon Soji

Ma’aikatar ta ce yakin Rasha da Ukraine ne ya zaburar da ita fara shirin.

Ma’aikatar Tsaron Poland ta ce rundunar sojinta za ta horas da ’yan kasar masu shekaru 18 zuwa 65 dabarun harbi da rike makami da sauran dabarun yaki.

Ma’aikatar ta bayyana hakan ne ranar Litinin, in da ta ce horon na kwana guda ne, kuma za a gudanar da shi a sansanonin sojojin 17 a dukkanin ranakun Asabar din watannin Oktoba zuwa Nuwamba.

Kazalika ta ce horon iya ’yan kasar ne kadai za su ci gajiyarsa, domin dabbaka shirinta na kara yawan adadin sojojin da take da su.

Kazalika, ma’aikatar ta ce yakin Rasha da Ukraine ne ya zaburar da ita fara shirin, kuma tuni ta fara kiraye-kiraye ga ma’aikatan gidajen aika wasika da su samu horon makamai, karkashin rundunar tsaron iyakokin kasar (WOT).

Sojojin Poland a halin yanzu sun kai 110,000, baya ga karin maza da mata 30,000 da aka yi cikin WOT din.

Haka kuma gwamnatin na da niyyar kara yawansu  zuwa 250,000, sai kuma WOT din zuwa 50,000.