✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PSG da Atletico Madrid sun tsallaka zagaye na gaba

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ci 3-2 a filin wasa na Anfield inda ta samu zuwa…

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ci 3-2 a filin wasa na Anfield inda ta samu zuwa zagaye na gaba a wasan kusa da na karshe a gasar.

A wasan da aka buga a karon farko dai Liverpool din ta sha kasha da ci 1-0 a filin wasan Atletico din.

Sai da aka kai ruwa rana a wasan inda Liverpool din ta ci kwallaye biyu rigis a mintuna na 43 da 94 bayan karin lokaci ta hannun ‘yan wasanta Gigi Wijnaldum da Roberto Firmino.

Atletico Madrid ta samu azama ne bayan da ta sako dan wasanta Marcos Llorente, inda ya farke kwallayen da aka ci Atletico din a mintuna na 97 da 105 a karin lokacin da aka yi.

Dan wasan gaban Atletico Madrid din Alvaro Morata, ne ya ci kwallo ta karshe da ta bai wa kungiyar ta birnin Madrid ta Sifaniya gurbi na gaba a gasar.

A gefe guda kuma, kungiyar kwallon kafa ta PSG ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Burossia Dortmund da ci 2-0 a filin wasa Parc De Prince, inda aka buga wasan babu ‘yan kallo.

A wasan farko dai Dortmund din ta samu nasara akan kungiyar ta Faransa da ci 2-1.

Zuwa yanxu dai kungiyoyin Atalanta, RB Leipzig, PSG da kuma Atletico Madrid ne suka samu gurbi a wasan kusa da na kusa da na karshe a gasar zakarun turai inda za’a kwashi ‘yan kallo a mako mai zuwa tsakanin kungiyar Manchester City da Real Madrid, Juventus da Lyon.

A wasu wasannin kuma za’a barje gumi tsakanin Barcelona da Napoli da kuma Bayern Munich da Chelsea.