Chelsea da PSG sun yanki tikitin zagayen daf da na karshe a gasar kofin Zakarun Turai | Aminiya

Chelsea da PSG sun yanki tikitin zagayen daf da na karshe a gasar kofin Zakarun Turai

Yayin haduwar Chelsea da FC Porto a ranar Talata
Yayin haduwar Chelsea da FC Porto a ranar Talata
    Ishaq Isma’il Musa da Abubakar Muhammad Usman

Kungiyar Chelsea FC mai buga gasar Firimiyar Ingila a birnin Landan, ta samu nasarar shallake zagayen daf da na biyun karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai.

A yammacin Talatar da ta gabata ce Chelsea ta mallaki gurbi a zagayen daf da na karshe duk da rashin nasarar da ta yi a wasan zagaye na biyu na matakin kwata final da ta fafata da FC Porto.

Chelsea ta yi rashin nasara a hannun FC Porto da ci 1-0, sai dai duba da kwallaye biyu da ta zira yayin wasansu na zagayen farko, ya bata damar wucewa matakin daf da na karshe wato semi final.

Haka ma PSG da ke buga gasar Ligue 1 a kasar Faransa, ta samu nasarar tsallakawa zagayen kusa na karshe a gasar cin kofin Zakarun Turan.

Haduwar da aka yi tsakanin PSG da Bayern a zagayen biyu na matakin daf da na biyun karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana

Taurarin Chelsea yayin da suka samu nasara a kan FC Porto yayin haduwarsu a zagayen farko na matakin daf da na biyun karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana

Kamar yadda ta kasance ga Chelsea, PSG ta sha duka a hannun Bayern Munich ranar Talata da ci 1-0, sai dai duk haka ta samu nasarar kai wa matakin semi final bisa la’akari da galabar da ta samu a kan Bayern da ci 3-2 yayin haduwarsu a zagayen farko na matakin daf da biyun karshe.

A yanzu dai kungiyoyin biyu za su jira wadanda za su samu nasara a wasanni biyu da za a fafata ranar Laraba tsakanin Real Madrid da Liverpool, sai kuma Borussia Dortmund da Manchester City a daya bangaren.