Daily Trust Aminiya - PSG ta dauki Wijnaldum daga Liverpool

Georginio Wijnaldum

PSG ta dauki Wijnaldum daga Liverpool

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sanar da daukar dan wasan tsakiya na Liverpool, Georginio Wijnaldum.

Dan wasan na kasar Netherlands ya rattaba hannu kan kwantaragin da zai dauke shi zaman shekara uku a kungiyar da ke Faransa.

Dan wasan wanda ya raba gari da Liverpool kyauta bayan karewar kwantaraginsa a karshen kakar wasanni ta bani, inda a yanzu sabon kwantaragin da ya kulla da PSG zai kare a ranar 30 ga watan Yunin 2024.

Wijnaldum mai shekara 30 a duniya na daya daga fitattun ’yan wasan kasar Holland da suka taka rawar gani a shekarun baya bayan nan.

Ya buga wa kasarsa wasanni 75 tare da zura kwallaye 22 sannan kuma ya taimaka wa kasar samun gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2014.

Gabanin haka, dan wasan ya wakilci kasar matakin ’yan kasa da shekara 17, 19 da kuma na ’yan kasa da shekara 21.

Karin Labarai