✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PSG ta raba gari da Pochettino

Kungiyar PSG ta sanar da batun kulla yarjejeniya da Christophe Galtier.

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta raba gari da kocinta, Mauricio Pochettino bayan shafe watanni yana jan ragamar horas da ’yan wasanta.

Fitaccen dan jarida wanda kuma ya shahara a kan fashin baki da tattara bayanan lamurran da suka shafi sauyin shekar ‘yan wasa, Fabrizio Romano ne ya tabbatar da hakan.

PSG ta kulla yarjejeniya da Christophe Galtier a matsayin mai horarwar da ya maye gurbin Pochettino.

PSG ta sanar da batun kulla yarjejeniya da Christophe Galtier a Talatar nan yayin taron manema labaran da zakarar ta Faransa ta kira.

PSG ta gudanar da gagarumin taron manema labaran a filin wasanta na Parc des Princes, inda ta yi amfani da damar don gabatar da Galtier a matsayin sabon mai horarwa.

Christophe Galtier, sabon mai horarwar da PSG ta dauka.

Tun a a ranar Litinin din ta da ta gabata ce kungiyar ta ki amsa tambayoyi game da gabatar da Galtier, duk da cewa wasu hotunan bidiyo sun nuna dattijon mai shekaru 55 ya isa kungiyar a yammacin ranar.

Tsawon makonni hudu kenan ana dakon sanarwar PSG game da sabon mai horarwa yayin da Pochettino da tawagar mataimakansa ke ci gaba da aiki.

Fabrizio ya tabbatar da cewa Galtier da ya shafe shekara guda yana horar da Nice, ya kulla kwantiragin shekaru 2 da PSG.

Pochettino ya raba gari da kungiyar bayan shafe watanni 18 tare da dage kofin Lig 1 duk da yake shi ma kamar wadanda suka gabace shi, ya gaza tabuka abin kirki a gasar cin Kofin Zakarun Turai.