✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PSG za ta dauko Zidane ya maye gurbin Pochettino

Masu kulob din na PSG na da burin lashe Gasar Zakarun Turai.

Kungiyar PSG ta kasar Faransa na gab da cimma yarjejeniya da Zinedine Zidane a matsayin sabon kocinta da zai maye gurbin Mauricio Pochettino.

A cewar gidan rediyon Europe 1, kungiyar na kan tattaunawa domin tsohon kocin na Real Madrid mai shekaru 49 ya koma PSG kafin sabuwar kakar wasanni.

Da Kamfanin dillancin labaran AFP ya tuntubi majiyar PSG, ta ki amincewa ko ta musanta rahotannin.

Pochettino dai yana da sauran shekara guda kan kwantiraginsa da PSG kuma ya jagoranci kungiyar da Qatar ke marawa baya samun nasara a gasar Ligue 1 a kakar da aka karkare, to amma Real Madrid ta fitar da su daga Kofin Zakarun Turai a zagaye na ‘yan 16.

Bayanai dai sun ta tabbatar da cewa masu kulob din na PSG na da burin lashe Gasar Zakarun Turai kuma kuma suna kyautata zaton daukar Zidane zai haifar musu da da mai ido duna da cewa ya jagoranci Real Madrid ta lashe Kofin Zakarun Turan kaka uku a jere tsakanin 2016 da 2018.

Zidane wanda tsohon dan wasa ne da ya lashe gasar Cin Kofin Duniya da Faransa a shekarar 1998, ya lashe Gasar Zakarun Turai a lokacin da yake dan wasa a Real a 2002.