✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PSG za ta tsawaita wa’adin Messi

Yarjejeniyar Messi za ta kare a watan Yunin 2023.

Kungiyar Paris Saint Germain ta shiga tattaunawar tsawaita kwantiragin fitaccen dan wasanta Lionel Messi na Argentina.

Luis Campos, mai ba da shawara kan harkokin kwallon kafa na PSG ne ya tabbatar a wannan Lahadin.

A halin yanzu dai yarjejeniyar Messi za ta kare a watan Yunin 2023.

Shugabannin PSG sun bayyana fatan Messi zai ci gaba da zama a kungiyar duk da cewa suna cikin tattaunawa.

Dan wasan mai shekara 35 wanda kuma ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai dole ne ya yanke shawarar abin da makomarsa za ta kasance.

Lamarin dai na zuwa ne ’yan makonni bayan ya kai ga lashe Gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar.

A shekarar 2021 ce Messi ya sauya sheka zuwa PSG kan yarjejeniyar shekaru biyu, bayan ya shafe tsawon shekaru a Barcelona.