✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Putin ya ce Rasha ba za ta ruruta wutar rikicin Ukraine ba —Macron

Macron ya bayyana haka ne a ziyararsa zuwa Kyiv, a yayin da Rasha ta musanta duk wata yarjejeniya da Faransa ta kulla kan rikicin Ukraine.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ba shi tabbacin cewa Rasha ba za ta kara ruruta wutar rikicin Ukraine ba.

Macron ya sanar da haka ne a ziyarar da ya kai Kyiv a ranar Talata, a daidai lokacin da fadar Kremlin kasar Rasha ta musanta cewa shi da Putin sun kulla yarjejeniya kan dakile rikicin na Ukraine.

Kakakin Gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov, ya ce “A halin da ake ciki yanzu, Rasha da Faransa ba za su iya cimma wata yarjejeniya ba”.

A lokacin ziyarar, Macron ya gana da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, a yayin da ake fargabar Rasha na shirin mamaye Ukraina.

Rasha dai ta girke dubunnan sojoji da kayan yaki a kusa da kan iyakarta da Ukraine, amma ta dage cewa ba ta da shirin kai hari kan Ukraine din.

Ita dai Rasha, so take ta samu tabbaci daga kasashen Yammacin Turai cewa NATO ba za ta amince da Ukraine da sauran tsoffin kasashen Soviet a matsayin mambobi ba, kuma kungiyar za ta dakatar da tura makamai tare da mayar da dakarunta daga Gabashin Turai.

Tuni dai Amurka da NATO suka ki amincewa da bukatun na Rasha a matsayinsu masu zaman kansu.

Macron ya ce yana da tabbacin za a iya dakile rikicin, sannan ya yi kira ga dukkan bangarorin da su kwantar da hankula.

Ya ce, Putin da Zelenskyy sun ba shi tabbacinsu na kiyaye ka’idojin yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a Minska a 2014, wadda ta ba da hanyar warware takaddamar da kasashen biyu suke ci gaba da yi.