✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Putin ya rattaba hannu kan dokar kara yawan sojojin Rasha zuwa miliyan 2

Matakin na zuwa ne bayan yakinta da Ukraine ta shiga wata na bakwai

Shugaban Rasha, Vladimir Putin a ranar Alhamis ya rattaba hannu kan wata doka da za ta kara yawan sojojin kasar zuwa miliyan biyu.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da yakin kasar da Ukraine ya shiga wata na bakwai.

Da wannan sabuwar dokar dai, yanzu sojojin Rasha za su kasance sama da mutum miliyan biyu.

Adadin ya kuma kunshi matasa masu yi wa kasa hidima miliyan 1.15, daga watan Janairun badi, a cewar sanarwar da kasar ta wallafa a wata kafar yada labaran gwamnati.

A shekarar 2017 ce Shugaba Putin ya kaddamar da kidayar sojojin kasar inda aka samu kusan mutane miliyan daya da dubu 900.

Sanarwar ta kuma zo ne a daidai lokacin da ake samun takun saka tsakanin Moscow da kasashen Yammacin Duniya da suka sanya wa Rasha takunkumi kan yakin da take yi a Ukraine.