✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Putin ya sa hannu kan dokar kwace jiragen kasashen waje

Rasha za ta kwace jiragen kasashen waje da ke kasarta domin amfanin cikin gida

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya sanya hannu kan wata sabuwar doka da ta ba wa hukumomin kasarsa ikon kwace jiragen kasashen duniya domin mayar da su na amfanin cikin gida a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Rasha (TASS) ya ce gwamnatin Shugaba Putin ta kafa dokar ce a matsayin ramuwar gayya ga takunkumai da kwace kadarorin Rasha da kasashen duniya ke yi saboda yakinta a Ukraine.

Tun kafin kafa sabuwar dokar wasu kamfanonin jiragen saman kasashen waje da Rasha ke haya suka daina aiki, bayan takunkuman da kasashen duniya suka kakaba mata.

Akwai bukatar gyare-gyare da jiragen fasinjan suke bukata, ammma dokar ta hana gudanarwa, wanda ya sa ake ganin dokar ba za ta yi tasiri sosai yadda ake zato ba.

Sabuwar dokar dai wani fito-na-fito ne tsakanin Putin da kasashen duniya da ke kokarin mayar da Rasha saniyar ware saboda mamayar da ta yi wa makwabciyarta Ukarine.

A makon jiya Gwamantin Amurka ta sanar cewa za ta daina sayen danyen mai da iskar gas daga Rahsa.

Shugaba Joe Biden ya kuma sanar cewa Amurka da wasu kasashe bakwai za su dauki matakan karya fifikon da Rasha ke samu fuskar cinikayya a matakin duniya.

Tuni wasu kamfanonin duniya da ke gudanar da harkokinsu a Rasha suka dakatar saboda rikicin, wanda yake ta shan suka.

A farkon makon nan Shugaban Kasar Ukarine, Volodymyr Zaelensky , a ganawarsa ta wayar tarho da Mista Biden, ya bukaci kasashen duniya su kara tsaurara wa Rasha ta hanyar hana jiragenta keta tekuna da kuma sanya takunkumi ga jami’an gwamnatinta.