✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Putin ya umarci jami’an nukiliyar Rasha su kasance cikin shirin ko ta kwana

Shugaba Putin ya zargi kasashen Yammacin duniya da daukar matakan nuna kyamar kasarsa.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci manyan kwamandojin tsaronsa da su sanya jami’an kula da makamin nukiliyar kasar cikin shirin ko ta kwana.

Wannan dai na zuwa ne bayan shugaba Putin ya zargi kasashen Yammacin duniya da daukar matakan nuna kyamar kasarsa.

Putin ya ce ya shaida wa Ministan Tsaron kasar da Babban Hafsa mai kula da rundunonin sojin Rasha da su sanya dakarun da ke kula da makaman nukiliyar cikin shirin yaki.

Shugaban ya shaida wa jama’ar kasar ta kafar talabijin cewar wadannan kasashen Yammacin duniya, bayan nuna kiyayya sun kuma sanya wa kasar haramtaccen takunkumin karya tattalin arziki, yayin da ya zargi manyan kasashen da ke cikin kungiyar NATO da kalamai masu zafi a kan kasarsa.

Tuni Ministan Tsaron kasar Shoigu ya amsa umurnin shugaban na sanya dakarun cikin shirin ko ta kwana.

Sai dai kasar Amurka ta zargi shugaban na Rasha da daukar matakan zafafa tashin hankalin saboda umurnin da ya bayar na saka dakarun kula da makaman nukiliyarsa cikin shirin ko ta kwana.

Mai magana da yawun fadar shugaba Jen Psaki ta ce sun saba ganin irin wannan matakin daga shugaban wanda ke kirkirar karya domin biyan bukatun kansa.

Ita ma Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta yi mummunar suka a kan wannan mataki wanda ta ce zai dada zafafa rikicin da ke gudana.

Sakataren Kngiyar Tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana ikirarin shugaba Putin a matsayin rashin hankali musamman ganin abin da yake faruwa yanzu haka a Ukraine.