✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Putin zai harba wa Ukraine makami mai guba —Biden

Biden ya gargadi Putin kan yunkurin harba makami mai guda kan Ukraine.

Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden, ya yi zargin cewa Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, na shirin harba makami mai guba zuwa Ukraine.

Biden ya gargade Putin cewa Kasashen Yamma za su dauki tsattsauran mataki a kansa muddin ya aikata hakan.

Kalaman Biden na zuwa ne a daidai lokacin da ita ma Kungiyar Tarayyar Turai ta ce a shirye take ta kara lafta takunkumi kan Rasha sakamakon mamayar da ta yi wa Ukraine.

Ma’aiktar Tsaron Amurka ta ce a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, jiragen yakin Rasha sun yi shawagi fiye da sau 300 da zummar karya duk wani lagon Ukraine.

Sabbin alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar Talata, sun nuna cewa sama da mutum miliyan 3.5 ne suka tsere daga Ukraine sakamakon yakin da kasashen biyu ke tafkawa a tsakaninsu.

A nasa bangaren kuwa, shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana son ganawa gaba da gaba da shugaban Rasha Vladimir Putin domin tattaunawar sullhu a tsakaninsu.

Zelensky, ya ce muddin ya samu wannan dama ta ganawar, to zai yi amfani da ita wajen bijiro wa takwaran nasa batutuwan da suka shafi kawo karshen wannan yakin.

Har wa yau, ya ce zai gabatar wa Putin bukatar gudanar da zaben raba gardama game da yankunan Crimea da Donbas da kasashen biyu suke takaddama a kansu.