✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: Birtaniya ta kora Senegal gida da ci 3-0

Moroko ce kadai kasar Afirka da ta rage kuma take neman zuwa Kwata-Fainal a gasar da ita ce ta farko a Yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasar Senegal ta fice daga Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022 bayan tawagar ’yan wasan Birtaniya ta lallasa ta da ci 3-0.

Yanzu Birtaniya ta shiga sahun kasashen da za a fafata da su a matakin Kwata-Fainal, bayan dan wasanta, Jordan Henderson ya zura kwallon farko a minti na 38, Harry Kane ya kara a minti 48, sannan Bukayo Saka ya zura ta uku a minti 57 a ragar Senegal.

Da wannan rashin nasara a wasan na ranar Lahadi, ta tabbata Senegal ta shiga sahun kasashen Afirka, Kamaru da Ghana cikin masu dawowa gida bayan an doke su a Matakin ’Yan 16.

Senegal ta yi wannan rashin nasara ne duk da hari 10 da ta kai gidan Birtaniya, wadanda biyu daga ciki ne kawai suka nufi raga, ragowar takwas kuma suka yi wani wajen.

A daya bangaren kuma, tawagar ’yan wasan Birtaniya ta kai hari takwas a gidan Senegal, inda ta yi nasara zura uku daga cikin hudu da suka nufi ragar.

Bayan doke Senegal zuwa Kwata-Fainal, Birtaniya za ta fuskaci Faransa mai rike da kofin gasar, wadda ke kokarin kafa tarihin zama kasar da ta kare kambunta a shekara 60 da suka gabata.

A tarihin Gasar Kofin Duniya na FIFA, Italiya ce kasar da ta fara kare kambunta na 1934 a 1938, sai Brazil da ta lashe kofin a 1958 ta kuma kare shi a 1962.

A halin yanzu dai Moroko ce kadai kasar Afirka da ta rage kuma take kokarin tsallaka matakin ’Yan 16 zuwa Kwata-Faina, inda za ta fafata da Spain a ranar Litinin, a gasar da ita ce ta farko a Yankin Gabas ta Tsakiya.