✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: Faransa ta kora Poland gida da ci 3-1

Kylian Mbappe ya zura kwallo biyu a ragar Poland, Faransa ta kai Kwata-Fainal, ta tisa keyar su Robert Lewandowski gida da ci 3-1

Tawagar ’yan wasan Poland za su koma gida bayan Faransa ta casa su 3-1, ta kuma tsallaka zuwa Kwata-Fainal a Gasar Kofin Duniya da ke gudana a Qatar.

Faransa, mai kokarin kare kambunta a gasar, ta lallasa Poland ne a wasansu na ’Yan 16 da aka buga a Filin Wasa na Al-Thumama a ranar Lahadi.

Dan wasan Faransa, Oliver Giroud ne ya fara zura kwallo a ragar Poland a minti 44 da fara wasan.

Daga baya a minti na 74, Kylian Mbappe ya sa kwallo ta biyu a ragar Poland.

A minti na 91 kuma, bayan karin lokaci, Mbappe ya kara ta uku — kwallonsa ta biyu a wasan.

Da haka yanzu Kylian Mpabbe mai shekara 23 na da kwallo 8 a tarihinsa na Gasar Kofin Duniya.

Kawo yanzu shi ne kuma dan wasan da ya fi cin kwallo a gasar bana, da kwallo biyar.

Ana cikin karin lokacin ne Robert Lewondoaki na Poland ya farke kwallo daya a minti 99, aka tashi 3-1.

Hakan dai na nufin yanzu Poland ta shiga sawun kasashen da suka nade buzunsu zuwa gida a gasar ta 2022.

A wasan na ranar Lahadi, Faransa ce ta yi kakagida wajen rike kwallo da kashi 47, Poland kuma 41, a yayin da suka yi kankankan a kashi 12.

Faransa ta kai hari 17 gidan Poland, kuma takwas daga ciki sun tafi daidai, a yayin da Poland ta kai hari 10, amma biyu daga ciki ne suka tafi daidai.

Nan gaba ake sa ran fara wasan Senegal da Birtaniya a zagaye na ’Yan 16.