✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar 2022: FIFA ta nada Sunday Oliseh a kwamitin kwararrunta kan Kofin Duniya

Dan wasan ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta nada tsohon dan wasan Najeriya, Sunday Oliseh, a cikin kwamitin kwararru na nazari, da kididdiga (EFI’S) a Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi Qatar.

Tsohon dan wasan ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.

Kwararren dan wasan ya saka hotonsa da na sauran ‘yan  kwamitin wadanda suka hada da Arsene Wenger da Klinnsman da Zaccheroni da Cha da Mondragona da kuma Zubi, duk tsoffin ‘yan wasan da suka yi fice.

Oliseh ya kuma saka hotonsa da na sauran ‘yan kwamitin kwararrun  yana mai cewa, “Za kuma mu kawo muku shiri kai tsaye ta hanyar shirin sauraro na podcast bayan kowanne wasa daga FIFA.”

Kwamitin zai yi aiki ne a karkashin shugabancin tsohon mai horaswa na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila, Arsene Wenger shi, kuma zai yi nazarin kowanne wasa ne da kuma samar da kiddigarsa da alkaluman yadda aka buga wasan, da yadda ‘yan wasan suka taka kwallon.

Ana sa ran hakan zai samar da cikakkun bayanai na shi wasan da ‘yan wasan da kuma yadda aka buga kwallon domin yin nazari ta hanyar na’urori da kuma fasahohi na zamani.

Sunday Oliseh tsohon dana wasa ne wanda ya buga wa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya na 1994 da 1998, ya kuma buga a gasar Olympic ta shekara 1996  a inda kasar ta ci lamabar zinare.