✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar 2022: Maroko ta yi waje da Spain a bugun fanereti

Maroko ta ba mara da kunya a karawarta da Sifaniya.

Kasar Maroko ta kora Kasar Sifaniya gida, bayan da ta doke ta a bugun fanereti a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar na 2022.

Sifaniya ta buga wasan zagaye na 16 ne da Kasar Maroka, a yammacin ranar Talata.

Kasashen biyu sun barje gumi na tsawon minti 120, wanda hakan ta sanya kasashen zuwa bugun fanereti.

Sai dai Sifaniya ta gaza zura kwallo ko daya a raga a bugun fanereti.

‘Yan wasanta; Sarabia, Carlos Soler da Sergio Busquet na daga cikin ‘yan wasan da suka zubar da bugun fanereti.

Ita kuwa Kasar Maroko ta buga fanereti hudu, ta cinye sannan ta zubar da guda daya.

Yanzu haka dai Sifaniya ta bi sahun kasashe irin su Japan, Senegal, Amurka, Poland da sauransu.