✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar 2022: Yadda kasar Maroko ta daga darajar Afirka

Tuni Maroko ta daga darajar Afirka a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Kasar Qatar.

Kasar Maroko ta bai wa mara da kunya a wasan da ta barje gumi da kasar Spain, wanda ta samu nasarar kora ta gida bayan an yi bugun fenareti.

Daga cikin kasashen Afrika hudu da suka samu gurbin zuwa Gasar Kofin Duniya da ake yi a kasar Qatar ta 2022, Maroko ce kadai ta kai bantentan ya zuwa yanzu.

Ragowar tawagar kasashe biyu da suka hada da Kamaru da Ghana sun gaza fitowa daga rukuninsu.

Kasar Senegal ce kadai ta fito, ita ma Ingila ta yi mata wankan jego da ruwan kwallaye uku rigis a raga.

Ita kuwa Maroko, da farko masu sharhi da hasashen wasanni ba su yi tsammanin za ta ba da tsaiko ga abokan karawarta ba.

A ranar Talata ce kasar ta buga wasa cikin hikima da bajinta da salo, inda ta kai wa Spain munanan hare-hare.

Tuni dai sauran magoya bayan kasashen Afirka suka shiga goyon bayan Maroko ganin irin rawar da ta taka na kora Spain din gida, wanda yanzu ake ganin za ta iya kafa tarihi a matsayin kasa ta farko idan har ta je matakin kusa da na karshe.

Kafin zuwa wannan mataki na kwata fainal, akwai kasashe irin su Kamaru, Senegal da kuma Ghana da suka taba zuwa wannan mataki.

Maroko ta kasance kasa ta hudu daga Afrika da ta taba zuwa wannan mataki a Gasar Kofin Duniya tun da aka fara ta a shekarar 1930, wato shekara 92 ke nan.