✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: ’Yan wasan Iran sun goyi bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Iran, Ehsan Hajsafi, ya bayyana goyon baya ga masu zanga-zangar adawa da gwamnatin kasarsa.

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Iran, Ehsan Hajsafi, ya bayyana goyon baya ga masu zanga-zangar adawa da gwamnatin kasarsa.

Ehsan Hajsafi ya jajanta wa mutanen da suka ji raunuka da iyalan wadanda suka rasu, a jajibirin ranar da kasarsa za ta fafata wasanta da farko da kasar Birtaniya a gasar Kofin Duniya.

Ehsan ya bayyana wa wa taron ’yan jarida cewa masu zanga-zangar, “Su sani cewa muna tare da su, domin abin da ke faruwa a gida babu dadin ji.”

A cewarsa, tawagar kwallon kafar na jajantawa ne a matsayinsu na muryar wadanda ake yi wa danniya a kasar Iran.

An shafe sama da wata biyu ana zanga-zangar a Iran kan jinin dokar sanya lullubi, tun bayan da wata matashiya mai shekara 22, mai suna, Mahsa Amini, ta rasu a hannun jami’an Hisbah, bayan tsare ta kan shigar da ta saba wa Musulunci.