✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: Zafin cin kwallon Moroko ya haddasa tarzoma a Belgium

Kasar Maroko dai ta lallasa kasar Belgium ce da ci biyu da da nema a gasar

Tarzoma ta barke a biranen Brussels da Amsterdam na kasar Belgium sakamakon cin da Maroko ta yi wa kasar a Gasar Cin Kofin Duniya da a ke yi a Qatar.

Magoya bayan Maroko ne sun fita kan manyan titunan Brussels da Amsterdam dauke da tutocin Morokon, cikin murna, suna wakoki tare da wasa motoci a ranar Lahadi.

Hakan aka ce ya fusata wasu ‘yan Belgium a inda suka far musu, wanda hakan ya haddasa tarzoma, bayan da wasu matasa da suka rufe fuskokin su da kyallaye suka rika jifan masu murnar da abin tartsatsin wuta a kusa da wata tashar jirgin kasa da ke birnin na Brussels.

A birnin Amsterdam na kasar kuwa, ‘yan sanda sun bayar da rahoton barnata dukiyar jama’a, da kuma kone wani babur wuta da kuma kwandunan zuba shara a kan titin birnin, an kuma tuntsurar da wata motar wani kamfani a kan titi.

“Masu tarzomar sun yi amfani da abubuwa masu saurin kama wuta, da abubuwan jifa, da kuma sanduna, suka kunna wuta kan hanya,” inji Kakakin Rundunar ‘Yan Sandar birnin, Ilse Van de Kee.

Rundunar ta ce ta tura jami’anta da yawa kan manyan tititunan biranen biyu domin fatattakar masu tarzomar, sannan ta kuma rufe wasu manyan hanyoyin zuwa wuraren shakatawa na baki masu yawon bude ido.

Magajin Garin birnin Phillipe Close, ya yi tir da tashin hankalin, sannan ya yi kira ga masu tarzomar da su kaurace wa wuraren shakawata na ‘yan yawon bude ido da kuma manyan kantuna.

Kasar Maroko dai ta lallasa kasar Belgium ce da ci biyu da da nema a gasar rukunin ‘F’ da ake yi a Qatar a karshen makon da ya gabata.