✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: Zakir Naik na halartar Gasar Kofin Duniya

Gwamnatin Qatar ta gayyaci Dokta Zakir Naik domin ya gabatar da majalisin wa'azi a yayin da ake Gasar Cin Kofin Duniya a kasar.

Fitataccen mai wa’azin Musulunci dan kasar Indiya, Dokta Zakir Naik na halartar gasar kwallon kafar na Cin Kofin Duniya da za a soma a Qatar a ranar Lahadi.

Hakan ta bayyana ne bayan fitar hotunan Dokta Zakir Naik bayan saukarsa a filin jirgin sama na Doha, babban birnin kasar Qatar a ranar Asabar.

Wasu bayanai sun nuna cewa mai Zakir Naik ya je Qatar ne a bisa gayyatar gwamanatin kasar na ya gabatar da wani majalisin wa’azi a yayin da ake gasar.

Qatar ta bijiro da wasu tsare-tsare na yada addinin Musulunci a yayin gasar Cin Kofin Duniya da ake sa ran mutum sama da mutane miliyan biyu da rabi za su halarta.

Wasu daga cikin tsare-tsaren sun hada da samar da wuraren Sallah da kuma wuraren alwala a filayayen wasa, abin da ba a taba yi ba a tarihin gasar a duniya.

Qatar ta kuma hana sayar da barasa a wuraren da za a buga wasannin.