✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2023: Muhimman abubuwa kan karamar kasa mai tarin arziki

Qatar na daga cikin kasashen Labarawa mafiya kankanta amma take kan gaba wajen arzikin mai da iskar gas

Qatar, karamar kasa mai dimin arzikin mai da iskar gas, ita ce mai masaukin bakin Gasar Kofin Duniya na 2023 kuma babbar kawar Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ga wasu muhimman abubuwa guda biyar da ya kamata ku sani game da kasar ta Qatar.

Karamar kasa

Qatar na daga cikin kasashen Labarawa mafiya kankanta — yawan al’ummanta miliyan 2.9 kuma yawancin ma’aikatan baki ne.

Ta kasance karkashin mulkin Birtaniya na tsawon shekaru 55 har zuwa 1971.

Sarkin kasar mai ci, Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, ya kama sarauta ne a 2013 bayan saukar mahaifinsa, Sheikh Hamad bin Khalifa Al-Thani.

A 2021 kasar ta gudanar da zaben ’yan majalisarta a karon farko.

Mai dimbin arzikin mai

Karamar kasar tana daya daga cikin kasashe mafiya arzikin gas a duniya.

Kasa ce mai karfin tattalin arziki da hannayen jari masu yawa.

Tana da kadarori a manyan kasashe irin su Birtaniya da Faransa da sauransu.

Rikicin diflomasiyya

Qatar ta fuskanci rikicin diflomasiyya tsakaninta da makwabtanta kasashen Larabawa na tsawon shekara uku da rabi (Yuni 2017 zuwa Janairu 2021) amma hakan bai yi mata illar a-zo-a-gani ba.

Kasar ta shiga dar-dar bayan bullar guguwar sauyi da neman dimokuradiyya a kasashen Larabawa.

Masarutar kasar ta goyi bayan haka amma ban da sauran sarakunan yankin Larabawa.

Wannan ya sa kasashen Saudiyya, Bahrain, Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa yanke hulda da Qatar tare da zargin ta da mara wa ta’addanci baya.

Saudiyya ta mika wasu bukatu ga kasar domin janye wariyar da ake nuna mata, cikin ciki har da rufe kafar yada labaranta ta Al-Jazeera, amma ta ki amincewa da bukatun.

Daga bisani Amurka ta shigo aka fitar da Qatar daga halin da ta tsinci kanta, daga nan suka zama kawaye.

Harkar wasanni

Qatar ba ta yi da wasa ba wajen kashe makudan kudade a fagen wasannin motsa jiki a gida da waje.

Ko a 2017 ta fitar da Yuro miliyan 222 inda ta sayi fitaccen dan wasan kwallon kafar nan, Neymar.

Ita ce kuma mai kungiyar kwallon kafar KAS, kana ta ba da sanarwar za ta mallaki hannun jari kusan kashi 22 harkokin wasannin motsa jikin kasar Portugal.

Kasar ta shirya gasar wasannin motsa jiki na kasa da kasa da dama da zummar daga darajarta a idon duniya.

Hakkokin jama’a

Tun bayan da ta nuna kwadayinta na karbar bakuncin Gasar Kofin Duniya, hankula suka koma kanta, musamman yanayinta da kuma batun hakkokin jama’a, musamman ga baki.

Rahotanni da dama sun nuna kasar ba ta damu da hakkokin ma’aikatan da suka mutu da wadanda suka ji rauni a bakin aiki ba, inda hukumomin kasar ke hana su hakkokinsu.

Ga azabtar da ma’aikata da kuma koran su daga kasar don sun gudanar da zanga-zanga kan rashin biyan su hakkokinsu.

Daga bisani, bayan sukar da ta sha daga bangarori daban-daban, gwamnatin kasar ta dauki matakin gabatar tsarin mafi karancin albashin da za a rika biyan ma’aikata.

Sannan ta janye dokar da ta bai wa iyayen gida ikon jujjuya ma’aikatansa yadda suka ga dama.