✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar na shirin sayen kungiyoyin Firimiyar Ingila uku

Tun a shekarar 2011 Qatar ta mallaki kungiyar PSG da ke Faransa.

Qatar na duba yiwuwar sayen wasu manyan kungiyoyi uku da ke buga gasar Firimiyar Ingila ko kuma saye wani sashe na su.

Kungiyoyi da kasar mai arzikin man fetur ke shirin saye sun hada Manchester United da Liverpool da Tottenham Hotspur.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan kasar ta fuskanci caccaaka a lokacin da ta yi ta fafutukar neman daukar nauyin Gasar Kofin Duniya ta 2022 da aka kammala kwana-nan nan.

An jinjina wa Qatar kan yadda ta dauki nauyin gasar ta cin Kofin Duniya mafi tsada a tarihin duniya.

Shafin Bloomberg ya ruwaito cewa, tuni Shugaban Hukumar Zuba Hannayen Jari a Wasanni na Qatar (QSI), Naseer Al-Khelaifi ya tattauna da shugaban kungiyar Tottenham, Daniel Levy kan yiwuwar sayen wani hannun jari mai tsoka na kungiyar ta London.

Kazalika Bloomberg ya ce, Qatar din na duba yiwuwar mallakar Manchester United da Liverpool baki dayansu.

A cewar Bloomberg, ta tattaro bayanan ta ne daga wani mutum da ya bukaci a sakaya sunansa, amma ya na cikin mutanen da suka halarci taron tattaunawa kan batun sayar da kungiyoyin ga Qatar.

Hukumar ta QSI ita ce ke da mallakin kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain da ke Faransa wadda ta siya a 2011.